News
Trending

An Mayar Wa El-Rufai Da Martani Kan Zargin Da Yakeyi Wa Wasu Daga Cikin Fadar Shugaban Kasa Masu Zagon Kasa Kan Tinubu.

Gwamnatin Najeriyata ta mayar da martani kan zarge-zargen da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi na cewa ”wasu mutane” a fadar shugaban ƙasar na ƙoƙarin daƙile nasarar ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

El-Rufai ya yi zargin ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels TV ranar Laraba, inda ya ce ”na yi imanin cewa akwai wasu a fadar shugaban asar da suke so mu fai zae, saboda ba su samu yadda suke so ba”

”Suna da nasu ɗan takarar, amma bai yi nasara a zaɓen fidda gwani ba, ina ganin har yanzu suna so mu faɗi zaɓe, kuma suna raɓe wa da burin shugaban ƙasa na ganin ya yi duk wani abu da yake jin daidai ne”, in ji El-rufai.

To sai dai ministan yaɗa labaran ƙasar Lai Mohammed, ya mayar da martani a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim-kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar, da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Lai Mohammed ya sake jajjada matsayin shugaban ƙasar na cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tabbatar da gudanar da sahihi kuma amintaccen zaɓe a ƙasar ba tare da yi wa wani alfarma ko daƙile wani ba.

Ya ƙara da cewa in ma akwai wanda yake yi wa wani ɗan takarar zagon ƙasa, to su a hukumace ba su san shi ba.

Advertisement
Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button