
Ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubukar ya ce bai kwana da shakkar babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
A lokacin tattaunawarsa da BBC Hausa, Atiku Abubakar ya ce bai taɓa jin tsoron fafatawa da wani ɗan siyasa a ƙasar ba.
Atiku Abubakar ya kuma ce sauran manyan ‘yan takarar shugabancin ƙasar biyu na jam’iyyun NNPP da LP ba sa tayar masa da hankali domin a halin yanzu ma suna kan tattaunawa da su domin yiyuwar haɗa kai a zaɓen da ke tafen.
Advertisement