News
CBN Ya Kara Kwana 10 Na Kin Ansar Tsofaffin Kudi

Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin takardun kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu.
Gwamnan Babban BankinGodwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan ɗaya da biliyan 900 na tsoffin takardun kuɗi, inda kuma ya ce saura naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsoffin takardun kuɗaɗen.
Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarni kuma mun samu daga shugaban ƙasa kamar haka: ƙarin kwanki 10 na karɓar tsofaffin takardun kuɗi daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabrairu, za a ci gaba da karɓar kuɗin daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.
Advertisement
2 Comments