Malaman SunnahNews
Trending

Dr Jameel Muhammad Sadis – Sarkin Dutse Bawan Allah

SARKIN DUTSE BAWAN ALLAH…!!!

Allah ya yi masa baiwar son ilimi da ma’abotansa tare da ruqo da addini. Natsuwa, dattako, sauqin hali, kawaici da karamci halaye ne bayyanannu a rayuwarsa.

Kana mu’amala dashi kana qara qaunarsa. Hasken fahimtar addini a bayyane yake a mu’amalarsa. Yana ciwon ajali amma yana kewar qiyamullaili (Sallar dare) wacce ya saba yi.

Na samu kusanci dashi ta sanadiyyar Malaminmu, d’an’uwa kuma amini Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu

Kwanakin baya mun zauna tsawon awa biyu, yana bayyana mun akwatin sirrin Nigeria. Ya sha mun kyautar kayan alfarma; Allah ya tufatar dashi alharirin Aljannah. Ameen.

Dan’uwana kuma aminina Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu ina yi maka ta’aziyyar rashin amini kuma masoyi. Allah ya lullubeshi da rahamarSa ya azurtashi da ceton manzon rahama S.A.W. ameen.

Advertisement
Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button