EntertainmentNews

Dr Jameel Muhammad Sadis Zaria – Fassarar Waqar (SHAYI)

Madallah da wannan abun sha wanda yake cikin wannan kofi mai daraja.

Akwai natsuwa da debe kewa lokacin kallon (jan shayi) mai daukar hankali.

Jikina har karkarwa yake yi idan na kalli mariqin kofin shayi. Ba ma wannan kawai ba Jama’a; begen kurbar shayi ya kan fizgo hannuna don daukar kofin.

Wani lokaci nakan samu kaina a cikin damuwa da rashin farin ciki. Amma da zarar na kurbi shayi sai in ji wasai; damuwar ta tafi.

Jama’a..!! matuqar kuna da rai toh kar kuyi sakaci da shan shayi. Allah ne kadai ya san abun da masu shan shayi suke ji na farin ciki da dadin rai.

Allah ya hada mu da shayin Jannatul Firdaus. Ameen.

NB: Jama’a kar fa ku dauka santi nake yi. A’a.. ina qoqarin bayyana darajar shayi neπŸ˜„

Jameel.

Advertisement
Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button