Malaman Sunnah
Trending

Dr Jameel Muhammad Sadis Zaria – Nasiha 4

Babban nasiha daga dr jameel muhammad sadis zaria inda yake cewa :

Kar ka ba ni labarin inda kaje a duniya ko wayewarka. Kar ka sanar da ni zurfin tuninka.

Kar ka fada mun yalwar iliminka. Duk zan fahimce su cikin sauqi ta hanyar dabi’unka da halayenka.

Dr Jameel Muhammad Sadis Zaria
@drjameelmuhammadsadis

Dabi’unka su ne jakadun wayewarka, iliminka da zurfin tunaninka.

Allah Ka azurtamu da kyawawan halaye. Ameen.

Idan ka lura da kyau za ka fahimci cewa masu yawan sukan mutane sun fi siffantuwa da aibu tattare dasu. Ko ba komai, aibun sukan mutane ma kawai ya isa zama babban aibu a rayuwa.

Abun mamakin shi ne ya suke mantawa da tarin aibinsu amma su shagala da na wasu…!!?.

Mallam Bahaushe ya yi gaskiya ” Laifi tudu ne, take na ka ka hango na wani”..!!

Jameel Muhammad Sadis

Advertisement
Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button