
Mune Dattawan Arewa Don Haka banajin Tsoron Kowani Dattijo – El-Rufai
Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, ya ce a matsayinsu na gwamnonin arewa za su yi iyakar kokari wajen ganin mulkin Najeriya, ya koma hannun mutanen kudu a zaɓe mai zuwa.
Cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, el-Rufai, ya ce “Duk wani zagon kasan da ake in sha Allahu zaben nan mun riga mun ci shi, kuma ba ja da baya za mu yi wannan yaki, za mu kuma kunyatasu mu nuna musu cewa mu ‘yan Arewa ba mutanen banza bane”.
Gwamnan na Kaduna ya ce, “Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewa, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mune shugabannin Arewa.”
“Don haka mun ja layi sannan mun lashi takobin idan Allah ya yarda za mu kunyata su.” In ji shi.
Cikin hirar tasa, el-Rufai, ya kalubalanci masu fakewa a bayan sabon tsarin canjin kuɗin Najeriya da manufar gurgunta ɗan takararsu na shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Ya ce,”Yawanci masu yin wannan abu ba ‘yan jam’iyya ba ne, mu muka yi jam’iyyar nan, mu muka yi yakin zabe, su kuma suka kwace gwamnati suke amfani da ita suna jin dadinta, sannan kuma suke yi wa jam’iyya zagon kasa suna yaudarar shugaban kasa.”
Gwamnan na Kaduna, ya ce idan ba zagon kasa ba, me yasa za a ce sun shekara takwas suna gwamnati sai yanzu kusan zabe za a bullo da batun sauya takardun da kuma batun karancin mai da ake fama da shi a kasa?
Ya ce, “Kamar yadda ake yada wa a kafafan sada zumunta cewa muna zargin mataimakin shugaban kasa da zagon kasa, sam ba ruwan farfesa Osibanjo, wannan abu da ake munafunci ne na mutanen Arewa saboda suna so su munafunce mu da mu gwamnonin Arewa muka ce muna so Mulki ya koma kudu.”
Gwamnan na Kaduna ya ce “Sun jima suna irin wannan bita da kullin kallonsu kawai muke don lokaci ya kusa, amma a fito karara ana ba wa shugaban kasa shawarar da za ta kada jam’iyya, dole ne mu taka musu birki, kuma wallahi za mu yi.”