BloggingEntertainmentMalaman SunnahNewsTech
Trending
Sirrorin maimaituwar lafazin (Al-kazib) har sau uku a wannan ayar tare da wasu fa’idoji – Dr jameel muhammad sadis

Wasu kalmomi a cikin AL-QUR’ANI suna maimaituwa sabo da dalilai da yawa. Dalilan suna iya bambanta daga aya zuwa wata.
Ga wasu daga cikin sirrorin maimaituwar lafazin (Al-kazib) har sau uku a wannan ayar tare da wasu fa’idoji a taqaice:
- Domin kowa ya fahimci cewa ita dai qarya; qarya ce ba a canza mata suna ko da kuwa an yi mata fenti, Kuma a ko ina aka yi ta sunanta dai qarya qarara.
- Lafazin (Al-kazib) na farko an yi matuqar qure fasaha a cikinsa. Dalili kuwa shi ne: an kwatanta aikinsu na halartawa da haramtawa a cikin addini a matsayin qure linzamin qarya. Kai ka ce ma qaryar duniya ba za ta zama qarya ba sai an hada da tasu. Ko kuma ma kace qaryarsu ita ce mai siffanta duk wata babbar qaryar da aka taba yi a duniya. Ko baka san qarya ba toh za ka fahimci cewa su ma qarya ta ne lamba daya.
- A larabci akwai kalmomi da yawa wad’anda ma’anarsu yake bayuwa ga (Qarya). Kamar:
(الْمَيْن)، (الفرية)، (الزور)، (الإفك)(الاختلاق) (البهتان) (الباطل)
da sauransu. Sai dai anan ba wata kalmar da za ta iya wakiltar (الكذب) kyakkyawan wakilci ta dace da fagen maganar; shi yasa aka maimaita (Al- kazib) )har sau uku. - Bugu da qari; A larabcin ALQUR’ANI duk lokacin da kalmar (افتراء) ko mai kama da ita ta hadu da kalmar (Qarya) toh kalmar (الكذب) ce take wakiltar kalmar qaryar ba wata kalmar ba. Misali:
- (وَلَكِنَّ الذِينَ كَفَرُوا يَفْتَرُونَ عَلى الله الكَذِبَ)
- (أَفْتَرى عَلى الله كَذِباً أمْ به جِنّة)
- وَمَا ظَنُّ الذِينَ يَفْتَرُون علَى الله الكَذِبَ يَوْمَ الْقِيامَة..)
- (قَدِ افْتَرَيْنا عَلَى اللهِ كَذِباً إنْ عُدْنَا فِي مِلَّتِكُم)
- (فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى الله كَذِباً ..)
Da makamantan wadannan ayoyin. Wannan shi ne sirrin maimata kalmar (Al-kazib) a waje na biyu da na uku.
- Lafazin (Qarya) na biyu da na uku duk an gwama su da kalmar (افتراء). Hakan yana fa’idantar da cewa qaryar da suke yi ba ta da asali kuma qagaggiya ce. Kuma basu da dalilin yin ta. Kawai sun yi ne da gangar don su kawo yamutsi a cikin addinin Allah da kuma nuna taurin kai. Yahudawa kenan da masu kama dasu.
Kadan daga cikin abun da Allah ya haskaka mun kenan. Na kauce ma ambaton wasu sabo da gudun tsawaita bayani. Wallahu A’alam.
Allah ya rubuta lada na musamman ga dan’uwa kuma masoyi Dr Kabir Asgar .
Kana da wasu haleyen da ko mutum bai yi niyya ba sai zuciyarsa ta qaunace ka amma ni tuni dama nayi niyya. 😁
Jameel Muhammad Sadis
Advertisement