EntertainmentNews

Taurarin fim din Pathaan: Shah Rukh Khan, Deepika Padukone da John Abraham

Sabon fim na Fitaccen dan wasan Indiya Shah Rukh Khan Pathaan, da ya fito ranar Laraba, ya mamaye kanun labaru a kasar Indiya a `yan makwannin nan.

Khan- yana cikin manya-manyan taurarin Indiya, da aka fi kauna kuma sha`awar da ake ta nuna masa ba a bar mamaki ba ce.

Mai farin jini, da ban dariya da ke da miliyoyin masu sha`awar fina-finansa a gida da kasashen ketare, akan kwatanta afton a matsayin dan wasan Indiya “da ya fi muhimmanci wajen fitar da al`adu”, wanda sunansa da ficensa suka zarce fina-finansa.

Masu kaunarsa, suna kiransa da Sarki Khan ko Sarki na fina-finan Indiya.

Kuma Pathaan shi ne fim na farko da ya yi bayan likimon da ya yi na shekara hudu.

Mai shekara 57 a duniya, ya sake yunkurowa a manya-manyan allunan majigi bayan matsaloli daban-daban da koma baya daya bayan daya da yake ta cin karo  da su a rayuwarsa ta kashin kansa da kuma ta sana`arsa, ciki har kama dansa Ason Aryan Khan a shekarar da ta gabata, a kan tuhume-tuhume na  karya na mallakar miyagun kwayoyi- daga bisani an janye tuhume-tuhumen – da kuma wasu fina-finansa da ba su fito da farin jini ba.

Gibin da likimon nasa ya haifar ya ja hankali ga Khan da kuma haddasa sa ido ba kadan ba, a kan wannan fim, wanda har ila yau jarumai irin su Deepika Padukone, daya daga cikin taurarin Indiya da suka fi yin suna, da John Abraham duk suka fito a cikinsa.

Advertisement
Advertisement

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button