
Ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga Babban Bankin ƙasar CBN da ya magance wahalhalun da ‘yan ƙasar ke fuskanta na ƙarancin sabbin takardun kuɗi a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da ofishin yaƙin neman zaɓensa ya fitar, Atiku ya yi kira ga Babban Bankin da ya gaggauta sake duba matakan da ya ɗauka, domin ya wadata al’umma da sabbin takardun kuɗin.
Yayin da yake yaba wa Babban Bankin kan sauraron koken talakawan ƙasar, tare da yin ƙarin wa’adin kwana 10 na amfani da tsoffin takardun kudin ƙasar, Atiku ya yi kira ga Babban Bankin da ya sake duba matakan da ya ɗauka domin tabbatar da cewa an samu wadatattun sabbin takardun kuɗin a cikin al’umma.
Advertisement